15 Satumba 2024 - 12:12
Yaman Ta Kai Hari Tel Aviv Da Makami Mai Linzami Na Ultrasonic ballistic / A Tsawon Kilomita 2,400 Cikin Kasa Da Mintuna 12.

Kakakin Rundunar Sojin Yaman: Zamu Sanya Makiya Suyi Nadamar Ranar Da Suka Kawo Mana Hari

Yaman ta kai hari Tel Aviv da makami mai linzami na ultrasonic ballistic / cikin tazarar kilomita 2,400 a cikin ƙasa da mintuna 12.

Kakakin rundunar sojin Yaman ya sanar da cikakken bayani kan harin makami mai linzami na musamman da sojojin kasar suka kai kan Tel Aviv a yau Lahadi inda ya kara da cewa wannan lamari ya faru a karon farko a tarihin makiya yahudawan sahyoniya.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya bayar da rahoto bisa nakaltowa daga Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran inda ya habarta cewa: a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau ranar Lahadi, "Yahya Sarii" ya sanar da cewa, harin da aka kai yau a birnin Tel Aviv an kai shi ne da wani sabon makami mai linzami na ultrasonic, wannan makami mai linzami ya kai ga inda akai hadafi sannan kuma na'urorin tsaron makiya sun kasa gane shi tare da dakile shi.

Ya jaddada cewa: Wannan makami mai linzami ya yi tafiyar kilomita 2,400 a cikin mintuna 11 da dakika 30, lamarin da ya haifar da firgici da tsoro ga yahudawan sahyoniyawan, sama da yahudawan sahyoniya miliyan 2 sun tsere zuwa matsuguni kuma wannan lamari ya faru a karon farko a tarihin kasar makiya Sahayoniya.

Kakakin rundunar sojin Yaman ya kara da cewa: An gudanar da wannan farmakin ne a cikin tsarin mataki na biyar, kuma sakamakon kokarin da sashen makami mai linzami na sojojin Yaman ya yi na fadada fasahar makami mai linzami ta yadda za mu fuskanci kalubalen fada da makiya yahudawan sahyoniya da kuma shawo kan duk wani cikas da tsarin tsaro na Amurka da Isra'ila a cikin teku da doron kasa da nufin cimma manufofinmu.

Saree ya ci gaba da cewa: Rikici na kasa da kasa, hare-haren wuce gona da iri na Amurka da Birtaniya da kuma tsarin leken asiri ba zai hana kasar Yamen cika aikinta na addini da 'yan Adamtaka da kuma kyawawan dabi'u na kare al'ummar Palastinu ba. A jajibirin zagayowar ranar farko ta farmakin " guguwar Al-Aqsa", ya kamata makiya yahudawan sahyoniya su yi tsammanin karin hare-hare da ayyuka na musamman a nan gaba.

A safiyar Lahadi ne majiyoyin labarai suka ba da rahoton cewa makami mai linzami ya fado kusa da birnin Tel Aviv sannan kuma gobarar wuta ta tashi bayan haka.

A cewar wadannan majiyoyin, an ji karar kararrawa a tsakiyar yankunan da aka mamaye da kuma garuruwa da matsugunai kimanin 20 a gabashi da kudancin Tel Aviv, kuma tashar 12 ta gidan talabijin na gwamnatin sahyoniyawan ta bayar da rahoton cewa "Daniel Hagari" kakakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila yace Sojojin sun ce an gano wani makami mai linzami a kasa a kan filin jirgin saman Lud da ke tsakanin Tel Aviv da Quds.

A halin da ake ciki kuma, ministan tsaron kasar Yemen ya gargadi kawancen Amurka da Birtaniya a daren jiya Asabar cewa, kwanaki masu zuwa za su zama abin mamaki da ba za a iya tantancewa ga makiya ba.

A cikin wani jawabi da ya yi, "Muhammed Al-Atafi" ya yi gargadi ga ƙawancen ƙasashe masu goyawa Amurka baya da cewa: Martanin da za mu yi wa makiya za su rikide zuwa mummunan mafarki mai ban tsoro da zai jefa amincinsu cikin hadari.

Ya kara da cewa: Muna gargadin makiyanmu cewa kwanaki masu zuwa za su zo da abubuwan mamaki da ba su zato ba.

Ministan tsaron kasar Yemen ya kara da cewa: Za mu mayar da martani da hannun karfe, ba za mu yafe ba, ba za mu manta ba, kuma za mu sa makiya su yi nadamar ranar da suka kawo mana hari.